Isa ga babban shafi
Wasanni

Kane ya amince da sauya sheka zuwa Real Madrid

Dan wasan gaba na Kungiyar Tottenham Harry Kane ya cimma yarjejeniya da Real Madrid kan sauya sheka zuwa gareta idan aka bude kasuwar ‘yan wasa ta gaba.

Dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane.
Dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane. Reuters/Paul Childs
Talla

Shahararriyar mujallar labaran wasanni ta kasar Spain 'Don Balon' ta rawaito cewa Harry Kane ya amince ya rattabawa Real Madrid hannu kan yarjejeniyar murza mata leda tsawon shekaru 5.

Sai dai an cimma matsayar ce tsakanin dan wasan da wakilan Real Madrid, yayin da a yanzu ya rage, tattaunawa tsakanin Madrid din da kuma Tottenham kan farashin Harry Kane.

An dai shafe watanni ana alakanta Harry kane da sauya sheka zuwa Real Madrid tun bayan da tauraruwarsa ta dada haskawa a fagen zura kwallaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.