"Tunusia ce kasa mafi kwarewa a fagen kwallon kafar Afrika"
Najeriya ta samu koma baya da mataki guda a jerin kasashen da suka fi kwarewa a fagen kwallon kafa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sabon sakamakon yana kunshe ne cikin rahoton da hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta saba fitarwa a kowane wata, wanda ta wallafa a jiya Alhamis.
Najeriya wadda a watan Janairu ke matsayin kasa ta 51 a duniya da maki 651, a yanzu ta koma kasa ta 52 a matakin kwarewa da maki 606.
Rahoton na FIFA ya bayyana kasar Tunisia a matsayin ta daya fagen kwallon kafar nahiyar Afrika, Senegal, Jamhuriyar Congo, Morocco, Masar da Kamaru sune a matakan na biyu zuwa shidda a jere, yayin da Najeriya ta ke a matsayi na bakwai.
Kasar Ghana ke biye da Najeriya a matsayi na 8, yayin da Burkina Faso da Algeria suke matsayin na tara da kuma goma.
A matakin duniya kuwa kasar Jamus ce kan gaba wajen kwarewa a kwallon kafa, biye da ita kuma Brazil da Portugal a matsayi na 2 da 3, sai kasar Argentina a matsayi na 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu