Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyoyin Najeriya sun yi bajinta a gasar zakarun nahiyar Afrika

Baki dayan kungiyoyin da wakiltar Najeriya a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Afrika Plateau United da kuma MFM FC ta Legas, sun samu nasarar kai wa zagaye farko na gasar daga zagayen sharar fage.

'Yan wasan kungiyar Plateau United da ke wakiltar Najeriya a gasar Zakarun Nahiyar Turai.
'Yan wasan kungiyar Plateau United da ke wakiltar Najeriya a gasar Zakarun Nahiyar Turai. Pulse.ng
Talla

A wasannin da suka buga a jiya, Plateau United ta samu nasarar lallasa Eding Sport ta kasar Kamaru da kwalaye 3-0 a Jos, wanda kuma a zagayen farko ta yi tattaki har Kamaru ta samu nasara kan su da 1-0.

Ita kuwa kungiyar MFM FC ta garin Legas ta karbi bakuncin Real Bamako ta Mali ce a filin wasa na Agege, inda ta samu nasara kanta da 1-0, a zagayen farko kuwa MFM ta yi kunnen doki ne 1-1, da Real Bamako a Mali.

A wasa na gaba Plateau United zata fafata ne da Etoile du Sahel na Tunisia a wata mai kamawa, yayin da ita kuma MFM FC zata jira wanda zata fafata da shi, tsakanin kungiyoyin MC Alger daga Algeria, ko kuma AS Otôho daga kasar Congo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.