Isa ga babban shafi
wasanni

Wenger ya sha alwashin lashe kofin Carabao

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya sha alwashin ganin ya lashe Lig Cup da aka fi sani da Karabawo yayin karawar da za su yi da jagora a gasar Firimiyar Bana wato Manchester City.

Karo na biyu kenan dai ana yin waje da Arsenal a karawar karshe ta lashe kofin na Carabao.
Karo na biyu kenan dai ana yin waje da Arsenal a karawar karshe ta lashe kofin na Carabao. Reuters/Michael Dalder
Talla

Wenger ya ce yana da kwarin gwiwar iya lashe kofin a karon farko yayin karawarsu da Man City din a Lahadin karshen makon nan.

Wenger wanda ya lashe kofin FA har sau 7, sau biyu kenan ana yin waje da shi a karawar karshe ta lashe kofin na Lig, a shekarar 2007 yayin karawarsu da Chelsea da kuma 2011 yayin karawarsu da Birmingham City.

Wenger ya ce za su zuba dukkanin ‘yan wasansu a ranar Lahadin don ganin sun faranta ran magoya bayansu.

Kalaman na Wenger dai na zuwa ne bayan shan kayen da suka yi a daren jiya alhamis a hannun Ostersunds da ci 2 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.