Isa ga babban shafi
Wasanni

Espanyol ta lallasa Madrid karon farko cikin sama da shekaru 10

Bayan buga wasannin La liga 5 cikin samun nasara a jere, Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Espanyol da kwallo daya mai ban haushi 1-0, a wasan da suka fafata a jiya, wanda Madrid din ta yi tattaki zuwa gidan Espanyol.

'Yan wasan kungiyar Espanyol, yayin da suke murnar zura kwallo a ragar Real Madrid cikin mintunan karshe na wasan La liga da suka buga.
'Yan wasan kungiyar Espanyol, yayin da suke murnar zura kwallo a ragar Real Madrid cikin mintunan karshe na wasan La liga da suka buga. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Dan wasan Espanyol Gerard Moreno ne ya jefa kwallon daya tilo a ragar Madrid yayinda aka shiga mintunan karshe.

Karo na farko kenan da Espanyol ta samu nasara akan Madrid cikin sama da shekaru goma, tun a watan Oktoban shekara ta 2007.

Cristiano Ronaldo bai buga wasan na jiya ba, saboda samun hutun fafatawa a wasan zakarun turai da zasu yi tattaki zuwa Faransa domin karawa da kungiyar PSG da suka lallasa ta da kwallaye 3-1 a Spain.

Muhimman ‘yan wasan Madrid da suka hada da Luka Modric, Toni Kroos, Marcelo da kuma Casemiro basu samu buga wasan na jiya da Espanyol ba, sakamakon fama da rauni.

A halin yanzu Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki 14 inda take a matsayi na daya a gasar La liga da maki 65, sai dai zata karar tazarar makin da ke tsakaninsu zuwa 17, idan ta yi nasara a wasan da zata yi tattaki domin fafatawa da kungiyar Las Palmas a ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.