rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Iraqi Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iraqi ta lallasa Saudiyya da ci 4 da 1

media
Rabon kasashen biyu da karawa tsakaninsu tun a shekarar 1979 inda Iraqin ta lallasa Saudiyar da ci 2 mai ban haushi. google.com

'Yan wasan Iraqi sun lallasa takwarorinsu na Saudiyya Green Falcons da ci 4 da 1 a wasan sada zumuncin da ya gudana tsakaninsu yau din nan a filin wasa na Basra mai daukar fiye da mutane dubu 60 a kasar ta Iraqi. Wasan dai shi ne irin sa na farko cikin kusan shekaru 40 tsakanin kasashen biyu.


Green Falcons na Saudiyya wadanda suka samu damar shiga gasar cin kofin duniya ta bana da za ta gudana a Rasha, su ne suka yi tattaki zuwa Iraqi wadda rabonta da makamancin wasan a cikin kasar ta tun a shekarar 1990.

Green Falcon din dai ta samu kyakkyawar tarba daga al'ummar ta Iraqi matakin da ake ganin zai iya kawo karshen takaddamar siyasar da ke tsakanin kasashen yau kusan shekaru 39.

Kusan za a iya cewa nasarar ta Iraqi kan Green Falcons da ci 4 da 1 tarihi ne ya maimaita kansa domin kuwa ko a wasan karshe tsakanin kasashen biyu a 1979 Iraqin ce ta lallasa Saudiyyar da ci 2 da nema.

Ko a litinin din da ta gabata ma dai Green Falcons din ta yi nasara kan Maldova da ci 3 da nema.

Yanzu haka dai ana wani gangamin tarbar ‘yan wasan Saudiyyar a Iraqi inda suke musu taken ‘‘Green Falcons gida kuka zo’’.