Isa ga babban shafi
Wasanni

Griezman ya zura kwallaye 4 a ragar Leganes

Dan wasan gaba na kungiyar Atletico Madrid Antonie Griezman ya ci kwallaye 4, a wasan da suka lallasa Leganes da kwallaye 4-0.

Antoine Griezmann yayin murnar zura kwallo ta uku a ragar Leganes.
Antoine Griezmann yayin murnar zura kwallo ta uku a ragar Leganes. REUTERS/Juan Medina
Talla

Karo na takwas kenan a jere, Atletico Madrid tana yamutsa Leganes a duk lokacin da suka fafata wasa.

A ranar lahadi da ta gabata ma dai kwallaye 3 Griezman ya ci a wasan da suka lallasa kungiyar Sevilla da kwallaye 5-2.

A halin yanzu tazarar maki 4 ce tsakanin Atletico da Barcelona a gasar La liga, wadda a yau zata yi tattaki don karawa da Las Palmas.

Ranar Lahadi mai zuwa Atletico Madrid zata yi tattaki zuwa filin wasan na Nou Camp don fafatawa da Barcelona, wasan da zai tantance yi wuwar Atletico ta samu damar sake matsar kungiyar ta Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.