Isa ga babban shafi
Wasanni

Bamu fidda ran lashe kofin gasar La liga ba - Zidane

Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya ce kungiyarsa bata fidda ran lashe kofin gasar La liga ba, duk da cewa abokiyar hamayyarsu Barcelona ta basu tazarar maki 15.

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane. Reuters/Juan Medina
Talla

A watan Fabarairu da ya gabata Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Espanyol da 1-0, karo na farko da Espanyol ta samu nasara akan Madrid cikin sama da shekaru 10, wasan da Madrid din ke matukar bukatar lashe wa domin dada rage tazarar da ke tsakaninta da Barcelona.

A halin yanzu wasanni 12 suka ragewa kowace kungiya ta buga a gasar ta La liga, wadda mai horar da Madrid Zidane ya bayyana kwarin gwiwar zasu iya kare kofin da suke rike da shi.

A yau Asabar Madrid zata karbi bakuncin kungiyar Getafe a filin wasa nan a Santiago Bernabeu, yayin da a gobe Lahadi, Atletico Madrid zata yi tattaki zuwa filin wasan na Nou Camp domin fafatawa da kungiyar Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.