Isa ga babban shafi
Wasanni

Madrid ta cancanci samun nasara akan mu - Emery

Mai horar da kungiyar PSG Unai Emery ya ce ba bin kunya bane a garesu, rashin nasara a hannun Real Madrid.

Mai horar da kungiyar Paris Saint-Germain Unai Emery.
Mai horar da kungiyar Paris Saint-Germain Unai Emery. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Emery ya bayyana haka ne bayan kammala wasan gasar zakarun turan na zagayen kungiyoyi 16, inda ya ce ba shakkah fitar da PSG a wannan matakin, abin bakin ciki ne, sai dai fa rashin nasara a hannun kungiya kamar Real Madrid ba abun alla wadai bane, domin kuwa sun cancanci samun wannan nasarar.

Cristiano Ronaldo da Casemiro ne suka ci wa Madrid kwallayenta 2, yayin da Edinson Cavani ya ci wa PSG kwallo daya.

Har yanzu kungiyar PSG ta gaza kai wa matakin wasan dab da na kusa da karshe a gasar Zakarun Turai, tun bayan da attajirin kamfanin wasannin kasar Qatar ya sayi kungiyar ta PSG a shekarar 2011.

Tun daga shekarar ce, PSG ta fara kashe makudan kudade, wajen sayen kwararrun ‘yan wasa zuwa yanzu, daga cikin shahararrun ‘yan wasan akwai, Neymar da PSG ta saya akan euro miliyan 222 daga Barcelona, da kuma Kylian Mbappe daga kungiyar Monaco, akan kudi euro miliyan 180.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.