Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA na gaf da daukar tattsauran hukunci akan Girka

Hukumar FIFA ta ce kowane lokaci daga yanzu zata iya haramtawa dukkanin kungiyoyin kwallon kafa na kasar Girka shiga wasannin kwallon kafa na duniya da ake bugawa a matakai daban-daban.

Herbert Hubel shugaban kwamitin FIFA da aka dorawa alhakin sa ‘ido akan hukumar kwallon kafa ta Girka.
Herbert Hubel shugaban kwamitin FIFA da aka dorawa alhakin sa ‘ido akan hukumar kwallon kafa ta Girka. Reuters
Talla

Herbert Hubel shugaban kwamitin FIFA da aka dorawa alhakin sa ‘ido akan hukumar kwallon kafa ta Girka, ya sahaidawa taron manema labarai cewa, daukar matakin zai zama tilas ne duba da yawaitar samun tashin hankali a mafi akasarin wasannin gasar kwallon kafa ta kasar Girkan.

Gasar kwallon kafa ta Girka, ta dade da yin suna wajen fama da matsalolin arrangama tsakanin magoya bayan kungiyoyi, da kuma cin da rashawa, wajen shiryawa kungiyoyi samun nasara a wasanni.

Matsala ta baya bayan nan da aka fuskanta ita ce wadda shugaban kungiyar PAOK FC Ivan Savvidis ya yi kundunbala cikin filin wasa dauke da bindiga domin nuna rashin amincewa da kwallon da kungiyar AEK Athens FC ta zurawa PAOK FC wadda ya ce satar fage aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.