Isa ga babban shafi
Wasanni

Kasashe 8 da za su fafata da juna a gasar Zakarun Turai

An fitar da jadawali kan yadda za a fafata tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a gasar Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 8.

Tambarin hukumar kwallon kafar Turai UEFA
Tambarin hukumar kwallon kafar Turai UEFA REUTERS/Jean Pierre Amet
Talla

Jadawalin  da aka fitar a birnin Nyon na kasar Suisse a wannan juma’a, na nuni da cewa

Liverpool - Manchester City

Juventus - Real Madrid

Séville - Bayern Munich

FC Barcelona - AS Roma

Za a yi karawar farko tsakanin kungiyoyin ne a ranakun 3 da 4 ga watan Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 10 da 11 ga watan na Afrilu.

A ranar 13 ga watan na Afrilu ne za a fitar da jadawalin kungiyoyin da za su hadu da juna a zagayen gaf da na karshe, wadanda kuma za su fafata da juna zagayen farko a ranakun 24 da 25 ga watan afrilu, kafin su sake haduwa a zagaye na biyu ranar 1 da 2 ga watan mayu.

Za a yi karawar karshe domin daukar kofin na Turai ne a ranar 26 ga watan mayu a birnin Kiev na kasar Ukiraine.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.