Isa ga babban shafi
Wasanni

An dakatar da Lyon a gasar UEFA

Hukumar gudanarwar gasar UEFA ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Lyon daga shiga wasanni bayan gano hannunta a yunkurin tayar da rikici a wasan da ya gudana tsakaninsu da CSKA Moscow ranar alhamis din mako jiya.

Tawagar kungiyar kwallon kafar Lyon.
Tawagar kungiyar kwallon kafar Lyon. Reuters / Murad Sezer Livepic
Talla

Club din na kasar Faransa dai dama yana fuskantar dakatarwar shekaru biyu tun a watan Afrilun 2017 bayan da ya haddasa tarzoma a wasan gab dana kusa dana karshe karkashin gasar Europa League, amma aka masa dakatarwar bayan bayar da hakuri tare da nuna ladabi.

Hukumar gudanarwar ta UEFA wadda ta ce za ta yi wani zama na musamman kan Club din na Lyon a ranar 31 ga watan Mayu, ta gindaya wasu sharudda da ta ce matukar Club din ya karya kafin wancan lokaci babu shakka zai fuskanci kwararan ladabtarwa ciki kuwa har da karin dakatarwa kan wadda yake fuskanta.

UEFA dai na zargin Lyon da nuna wariyar launin fata, yin jifa matukar aka yi nasara akansu, baya ga kankane wuraren zama tare da hana magoya bayan kungiyar da suke wasa da ita samun sukuni.

Lyon wadda ta sha kaye a hannun CSKA Moscow ita ke a mataki na 4 a teburin Ligue 1, tazarar maki biyu tsakaninta Marseille, haka zalika tana da sauran wasanni 3 manya da za su bata damar karawa a gasar zakarun Turai.

Haka zalika Lyon ita ke a matsayin ta 4 yanzu haka a gasar Europa League da ke ci gaba da gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.