rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Najeriya Poland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Wasanmu da Najeriya darasi ne babba"

media
Dan wasan gaba ba Poland kuma kaftin, Robert Lewandowski. Reuters

Dan wasan gaba na kasar Poland Robert Lewandoski, ya wasan sada zumuncin da suka yi rashin nasara a hannun Najeriya da 1-0, zai zama darasi a garesu, yayin da suke tunkarar halartar gasar cin kofin duniya a Rasha.


Lewandoski wanda ya ci wa kasarsa kwallaye 9 a wasanni 6, ya bayyana haka ne bayan kammala wasan sada zumuncin da suka fafata a ranar Juma’a.

Dan wasan ya kara da cewa kamata ya yi su ‘yan wasan na Poland su samu nasara akan Najeriya, domin kuwa a bayyane take, ‘yan wasan na Najeriya sun gaza tabuka abin azo a gani, wajen samawa kansu hanyoyin zura kwallaye a ragarsu.

Shi ma a nashi bangaren, mai horar da tawagar kwallon kafar Najeriya, Gernot Rohr ya ce akwai bukatar ‘yan wasansa su kara nutsuwa da yin taka tsantsan a wasannin da zasu tunkara a nan gaba, duk da cewa sun samu nasara akan Poland, kasa ta 6 a matakin mafi kwarewa a fagen kwallon kafa a duniya.

Rohr ya ce samun nasara akan kasashe kamar Argentina da Poland a wasannin sada zumunci ba shi bane zai bai wa Najeriya damar lashe kofin gasar kwallon kafa ta duniya ba.