Isa ga babban shafi
Wasanni- Rasha

FIFA ta bayyana sunayen alkalan gasar cin kofin Duniya

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta bayyana sunayen alkalan wasa 36 da mataimakansu 63, da zasu lura da wasannin gasar cin kofin duniya ta wannan shekara da za’a yi a Rasha.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

Daga cikin jami’an da FIFA ta zaba, akwai alkalan wasa daga nahiyar Afrika guda 6, wadanda suka kunshi, Abid Medhi daga Algeria, Diedhiou Malang daga Senegal, sai kuma Gassama Bakary daga kasar Guinea.

Sauran alkalan wasan sun hada da Sikawe Janny daga Zambia, Tessema Bamlak daga Habasha, sai kuma Grisha Ghead na kasar Masar.

Hukumar ta FIFA ta kuma zabi mataimakan alkalan wasa 10 daga nahiyar ta Afrika, daga kasashen, Morocco, Sudan, Burundi, Angola, Algeria, da Tunisia, sai kuma Kenya, Afrika Ta Kudu, da kuma kasar Senegal da aka dauki mutane 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.