Isa ga babban shafi
Wasanni

Nahiyar turai zata yi kewar Ibrahimovic - Mourinho

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya bayyana tsohon dan wasansa Zlatan Ibrahimovic a matsayin gwarzon da kwallon kafar nahiyar turai zata yi kewar bajintarsa.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho tare da tsohon dan wasansa Zlatan Ibrahimovic.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho tare da tsohon dan wasansa Zlatan Ibrahimovic. Reuters
Talla

Mourinho ya bayyana haka ne yayin da yake yiwa Ibrahimovic bankwana bayan sauyin shekar da ya samu daga United zuwa LA Galaxy da ke kasar Amurka.

A kakar wasa ta farko da ya yi a United Ibrahimovic ya ci wa kungiyar kwallaye 28, kafin daga bisani ya samu rauni, yayin wasan gaf da kusa da na karshe a gasar Europa cikin watan Afrilu da ya gabata, inda suka fafata da kungiyar Anderlecht.

Sai dai bayan warkewa daga ranin kwallo daya kawai, Ibrahimovic mai shekaru 36, ya samu ci wa Manchester United a wasan da suka yi da kungiyar Burnley cikin watan Nuwamban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.