Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta ki amincewa da rage hukuncin Oscar Pistorius

Babban kotun Afrika ta kudu ta yi watsi da bukatar Oscar Pistorius na daukaka kara kan hukuncin daurin shekaru 13 da aka yanke masa a gidan yari.Pistorius dai na neman Kotun ta rage wa'adin da aka sanya masa yayin shari'ar da ta gudana a watan Nuwamba.

Tsohon zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius yayin da ya gurfana gaban kotu kan kisar budurwarsa Reeva.
Tsohon zakaran tseren nakasassu Oscar Pistorius yayin da ya gurfana gaban kotu kan kisar budurwarsa Reeva. REUTERS/Ihsaan Haffejee/Pool
Talla

Tsohon zakaran wasan tseren bangaren nakasassu Oscar Pistourius na bukatar kotun kundin tsarin mulkin kasar ne ta yi duba kan hukuncin daurin shekaru 13 da aka kara masa a watan Nuwamban bara kan kisan budurwasa Reeva Steenkamp da gan-gan a shekarar 2013.

A cewar kotun batun bai shafi kundin tsarin mulki ba.

A shekarar 2012 dai Pistorius shi ne ya zo na daya a gasar tseren da ta gudana a London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.