Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ta kai matakin gaba a gasar zakarun Turai

A karon farko cikin shekaru 10, kungiyar kwallon Kafa ta Liverpool ta tsallaka matakin wasan dab da na karshe bayan ta doke Manchester City da ci 2-1 a zagaye na biyu na fafatawar da suka yi a jiya Talata.

Mohammed Salah ya ci wa Liverpool kwallaye 39 a wannan kaka
Mohammed Salah ya ci wa Liverpool kwallaye 39 a wannan kaka REUTERS/Phil Noble
Talla

Ko da yake da fari Manchester City ta nuna bajinta, in da ta yi kokarin farke kwallaye uku da Liverpool da zura ma ta a zagayen farko da suka yi a makon jiya, in da a cikin minti biyu Raheem Stareling ya bada kwallon da Gabriel Jesus ya jefa a ragar Liverpool.

Sannan kuma Bernardo Silva ya kai wani kyakkyawan hari gidan Liverpool amma hakarsa ba ta cimma ruwa, in da kwallon ta daki karfe, lamarin da ya haifar da fargaba ga Liverpool.

Sai dai fa a minti na 56, Mohammed Salah na Masar ya farke kwallon da Jesus ya jefa a raga, yayin da Roberto Firmino ya kara ta biyu a minti na 77.

Yanzu haka Mohammed Salah na da kwallaye 39 da ya jefa a raga a wannan kakar, yayin da ya taimaka wajen zura kwallaye 11.

A ranar Jumma’a mai zuwa ne Liverppol za ta san kungiyar da za ta kara da ita a matakin wasan dab da na karshe, wato bayan hukumar UEFA ta fitar da sabon jadawali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.