Isa ga babban shafi
wasanni

Real Madrid ta tsallake rijiya da baya

Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta tsallake rijiya da baya a karawar da ta yi da Juventus a gasar zakarun nahiyar Turai bayan Christiano Ronaldo ya ci ma ta kwallo daya ta hanyar bugun fanariti a minti na 97.

Christiano ronaldo ya fid da Real Madrid kunya a wasanta da Juventus
Christiano ronaldo ya fid da Real Madrid kunya a wasanta da Juventus REUTERS/Paul Hanna
Talla

Sai dai wannan fanaritin ya haifar da cece-kuce, in da wasu musammam magoya bayan Juventus ke caccakar alkalin wasan da ya bada damar bugun na daga kai sai mai tsaren gida.

Alkalin wasan daga Ingila, Michael Oliver ya bada fanaritin bayan Mehdi Benatia na Juventus ya hana Lucas Vazquez na Madrid zura kwallo bayan ya kawo ma sa hari ta baya a dab da gida.

Alkalin wasan ya kuma bai wa mai tsaren ragar Juventus, Gianluigi Buffon jan kati bayan ya yi jayayya da shi kan hukuncin da ya dauka, kuma ana ganin wasansa na karshe kenan a gasar cin kofin zakarun Turai.

Buffon da ake saran ritayarsa  na ba da jimawa ba, ya buga gasar zakarun Turai har sau 125 amma bai taba lashe kofin gasar ko sau da ya ba.

A martanin da ya mayar, Ronaldo ya ce, bai ga dalilin da ya sa ‘yan wasan Juventus ke bore ba saboda wannan bugun fanaritin da aka ba shi.

Yanzu haka dai Real Madrid mai rike da kambi ta shiga matakin gaba a gasar, in da za ta hadu da ko dai Liverpool ko Bayern Munich ko kuma Roma.

A gobe Jumma’a ake saran fitar da jadawalin wadannan kungiyoyi hudu da suka saura a gasar ta zakarun Turai.

Ita ma dai Bayern Munich ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Sevilla, amma duk da haka ta tsallaka matakin gaba na kasar saboda kwallaye 2-1 da ta fara zura wa a ragar Sevilla a makon jiya.

A karon farko kenan cikin wasanni 22 da ta yi a gidanta a gasar zakarun Turai da Bayern Munich ta gaza zura kwallo.

A bangare guda, Bayern Munich ta tsawaita kwantiragin Franck Ribery da shekara guda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.