Manchester City ta lashe kofin firimiyar Ingila
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin gasar firimiyar Ingila bayan abokiyar hamayyarta, wato Manchester United ta sha kashi a hannun West Brom da ci daya mai ban haushi.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka Manchester City ta bai wa Manchester United wadda ke a matsayi na biyu a teburin gasar ta firimiya tazarar maki 16 duk da cewa akwai wasanni biyar da suka rage.
A karo na uku kenan da Manchester City ke lashe kofi a cikin kakanni bakwai, amma a karon farko kenan ta dauki kofin firimiyar a karkashin kocinta Pep Guardiola.
Ko da yake Guardiola ya lashe kofunan firimiya a Spain da Jamus har ma da kofuna biyu a gasar zakarun nahiyar Turai tare da Barcelona.
Manchsester City dai ta nuna bajinta a gasar firimiya ta bana, in da jefa kwallaye 93 a raga, yayin da ta sha kashi sau biyu kacal, amma Liverpool ta yi waje da ita a gasar cin kofin zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu