rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mourinho zai ajiye Pogba da Herrera a banci

media
Kocin Manchester United, Jose Mourinho REUTERS/Peter Powell

A yayin da Manchester United ke shirin karawa da Tottenham a matakin wasan dab da na karshe a gasar FA, kocin kungiyar, Jose Mourinho ya ce, zai ajiye ‘yan wasansa da suka gaza tabuka abin kirki a wasan da suka sha kashi a hannun West Brom a banci.


A ranar Lahadin da ta gabata ne, West Brom dai ta yi wa Manchester United ci daya mai ban haushi a Old Trafford a gasar firimiyar Ingila, abin da ya bai wa Manchester City damar lashe kofin gasar cikin sauki.

Mourinho ya ce, yanayin taka leder dan wasa ne zai zame masa ma’aunin zabar sa ko kuma ajiye shi a banci, yayin da ya jaddada cewa, babu makawa, wasu daga cikin yaransa da suka buga fafatawarsu da West Brom ba su da wuri a karawar da za su yi da Tottenham a ranar Asabar a gasar ta FA a Wembley.

Manchseter United dai ba ta kammala karawarta da West Brom ba da Ander Herrera da ke buga tsakiya da kuma Paul Pogba wanda aka sauya a minti na 58.

A cewar Mourinho, Pogba ya fi kowa tsindima cikin tsaka mai wuya domin har katin gargadi ya samu a fafatawar.