Isa ga babban shafi
wasanni

'Yan wasan Roma ba za su sassauta wa Salah na Liverpool ba

Dan wasan Liverpool da tauraronsa ke hasakawa, Mohamed Salah zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa wato Roma a matakin wasan dab da na karshe a gasar zakarun Turai, yayin da kocinsa, Jurgen Kloop ke ganin cewa, dan wasan ba zai samu sassauci daga ‘yan wasan Roma a  fafatawar ta yau.

Mohamed Salah ya zura kwallaye 41 a kakar bana.
Mohamed Salah ya zura kwallaye 41 a kakar bana. REUTERS/Andrew Yates
Talla

Salah ya zura kwallaye 34 a wasanni 83 da ya buga a lokacin da yake taka leda a Roma a gasar Serie A kafin daga bisani ya koma Liverpool a kakar da ta gabata a kan farashin Pam miliyan 34, yayin da ya ci wa Liverpool kwallaye 41 cikin wasanni 46 da ya guga ma ta.

A karon farko kenan da Salah dan asalin Masar zai kara da tsohuwar kungiyar tasa.

A karon farko  tun shekarar 2007, Liverpool na fatan kai wa matakin wasan karshe a gasar ta zakarun Turai, yayin da wasu ke ganin cewa, mawuyaci ne ba ta yi waje da Roma a gasar ta bana ba.

Sai dai kuma ita ma Roma na iya bada mamaki, musamman idan aka yi la’akari da rawar da ta taka wajen fitar da Barcelona daga wannan gasa a bana.

A gobe ne ita ma Bayern Munich za ta fafata da Real Madrid mai rike da gambin gasar ta zakarun Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.