rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Djokovic ya fice daga gasar Barcelona Open

media
Shahararren dan wasan kwallon tennis Novak Djokovic. Reuters

Shahararren dan wasan kwallon Tennis na duniya Novak Djokovic wanda ya taba rike kambun mafi kwarewa a duniya, ya yi fitar bazata daga gasar Tennis ta Barcelona Open a zagaye na biyu.


Djokovic dan kasar Serbia ya fice daga gasar ne bayan da Martin Klizan dan kasar Slovakia kuma dan wasan tennis na 140 a duniya ya lallasa Djokovic din da 6-2, 1-6 da kuma 6-3 a ranar Laraba.

A baya bayan nan dai Djokovic ya gaza kai wa ko da matakin zagaye na uku a dukkanin wasanni daban daban da ya shiga guda 5, duk da cewa yana kokarin maido da karsashin da yake da shi kafin samun rauni a gwiwar hannunsa na dama.

Shi kuwa Rafeal Nadal dan Spain ya samu kai wa ga zagaye na uku a gasar ta Barcelona Open bayan lallasa Roberto Carballes takwaransa daga Spain din da kwallaye 6-4 da kuma 6-4.