Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho yayi nadamar rashin kyakkyawar alakarsa da Wenger

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho, ya bayyana yin nadamar yadda a wasu lokuta ya rika sukar takwaransa na Arsenal Arsene Wenger, tare da nuna masa wasu halaye da ke fayyace tsantsanr adawar da ke tsakaninsu.

Mai horar da Chelsea Jose Mourinho (dama) da takwaransa na Arsenal Arsene Wenger (hagu) yayinda da alkalin wasa Martin Atkinson ya shiga tsakaninsu yayin wasa tsakanin Arsenal da Chelsea a filin Stamford Bridge. Oktoba 5, 2014.
Mai horar da Chelsea Jose Mourinho (dama) da takwaransa na Arsenal Arsene Wenger (hagu) yayinda da alkalin wasa Martin Atkinson ya shiga tsakaninsu yayin wasa tsakanin Arsenal da Chelsea a filin Stamford Bridge. Oktoba 5, 2014. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Mourinho ya bayyana nadamar ce, yayin da yake shirin tunkarar wasan da zasu fafata da Arsenal a filin wasa na Old Trafford ranar Lahadi mai zuwa.

Tun a shekarar 2004 aka fara hamayya tsakanin masu horarwar biyu, bayan da Mourinho ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan Chelsea.

A bayan dai Mourinho yana bayyana Wenger a matsayin kwararre wajen samun rashin nasara, yayinda shi kuma Wenger ke kiran Mourinho da sunan sakarai.

A watan Oktoban shekara ta 2014, masu horarwar, wato Wenger da Mourinho sun kusa baiwa hammata iska a wani wasa da aka buga tsakanin Chelsea da Arsenal, daya daga cikin batutuwan da a yanzu Mourinho ke bayyana nadama akan faruwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.