Messi ya zarta Salah wajen zura kwallaye a nahiyar turai
Lionel Messi ya zarta dan wasan Liverpool Muhammad Salah wajen zama dan wasa mafi yawan zura kwallaye a tsakanin takwarorinsu na nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Kwallaye uku da Messi ya ciwa Barcelona a wasan da suka lallasa Deportivo Lacurona da kwallaye 4-2 ne suka bashi damar samun maki 64, bayan cin jimillar kwallaye 32, yayinda kuma yake da sauran wasanni 4 da zai buga a gasar la Liga.
Shi kuwa Muhammad Salah a halin yanzu, yana da yawan kwallaye 31 da maki 62, yayinda kuma ya rage masa wasanni 2 da zai buga a gasar Premier, sai kuma wasa guda a gasar cin kofin zakarun turai.
Cristiano Ronaldo shi ne dan wasa na karshe daga gasar Premier ta Ingila da ya lashe kyautar mafi yawan kwallaye bayan zura 31 a lokacin da ya taimkawa Manchester United lashe kofin kakar gasar ta Premier na shekarar 2007/2008.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu