Isa ga babban shafi

"Sake lashe kofin zakarun turai baya cikin sharadin rike mukamina"

Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane, ya ce sake jagorantar kungiyar wajen lashe kofin gasar zakarun turai karo na uku a jere, bashi da wata alaka da yiwuwar cigaba da rike mukaminsa, ko kuma rabuwa da kungiyar ta Madrid a karshen kakar wasa ta bana.

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane. Reuters
Talla

Rashin samun nasarori kamar yadda aka saba a wasannin La liga shi ne babban dalilin ya sa wasu ke ganin ba lallai bane Zinedine Zidane ya cigaba da horar da Madrid, bayan karewar kakar wasa ta bana.

A zagayen farko na wasan kusa dana karshen gasar zakarun turai Madrid ta samu nasara akan Bayern Munich da kwallaye 2-1.

Bayern Munich dai zata buga wasan na yau ba tare da dan wasanta Arjen Robben ba, sakamakon raunin da ya samu a zagayen farko na wasan da suka yi a Jamus.

Madrid ta lallasa Bayern Munich a wasanni 6 da suka fafata a baya, na gasar cin kofin na zakarun turai, rashin nasara mafi tsawo ba kungiyar ta Bayern Munich ta taba fuskanta daga wata kungiya guda a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.