Isa ga babban shafi
Wasanni

Ulreich ya nemi afuwar magoya bayan Bayern Munich

Mai tsaron gida na kungiyar Bayern Munich Sven Ulreich, ya nemi afuwar magoya bayansu, bisa kuskuren da ya tafka, wanda ya baiwa Real Madrid damar fitar dasu daga gasar zakarun turai a wasan kusa dana karshe da suka buga ranar Talata a Spain.

Mai tsaron gida na kungiyar Bayern Munich Sven Ulreich bayan kammala wasa da Real Madrid a Santiago Bernabeu, inda ya tafka kuskuren da ya bai wa Ream Madrid fitar da su daga gasar zakarun turai a wasan kusa dana karshe.
Mai tsaron gida na kungiyar Bayern Munich Sven Ulreich bayan kammala wasa da Real Madrid a Santiago Bernabeu, inda ya tafka kuskuren da ya bai wa Ream Madrid fitar da su daga gasar zakarun turai a wasan kusa dana karshe. REUTERS/Juan Medina
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Ulreich ya ce ba zai iya bayyana girman bakin cikin da ya riske shi ba, sakamakon wannan kuskure.

Ulreich ya gaza tare bashi kwallon da mai tsaron baya Corentin Tolisso ya bashi, damar da dan wasan gaba na Real Madrid Bezema ya samu wajen jefawa kungiyarsa kwallonta ta 2 a ragar Munich cikin sauki.

Ulreich ya samu damar shiga tawagar farko ta ‘yan wasan Bayern Munich ne, bayan da mai tsaron gida na kungiyar na farko Manuel Neuer ya samu rauni a watan Satumban shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.