rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barcelona ta gana da wakilin Griezmann na Atletico

media
Antoine Griezmann na Atletico Madrid REUTERS/Juan Medina

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya ce, ya gana da wakilin Antoine Griezmann a dai dai lokacin da ake rade-rdin kowar dan wasan Barcelona daga Atletico Madrid a wannan kaka.


A cikin watan Janairun da ya gabata ne, Barcelona ta musanta batun cimma yarjejeniyar siyan dan wasan mai shekaru 27.

Atletico Madrid ta kai wa hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA karar Barcelona bisa tinkarar ta ba bisa ka’ida ba don siyan dan wasan a cikin watan Disamban bara.

Sai dai shugaban na Barcelona a wata hira da aka yi da shi da tashar radiyon RAC1 ya ce, lallai ya gana da wakilin Griezmann a cikin watan Oktoban da ya gabata, amma babu wani abu da ya biyo bayan ganawar.

Barcelona dai na bukatar karfafa ‘yan wasanta na gaba masu zura kwallaye.