rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bayern Munich ta tsawaita kwantiragin Ribery

media
Franck Ribery zai ci gaba da zaman a Bayern Munich REUTERS/Albert Gea

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta tasawaita kwantiragin dan wasan tsakiyarta, Franck Ribery da shekara guda.


Wannan na zuwa ne a yayin da ake rade-radin cewa, Bafaranshen dan wasan mai shekaru 35 zai raba gari da Bayern Munich da ta kasance zakarar gasar Bundesliga a cikin wannan kaka.

Dan wasan ya zura kwallaye 117 a wasanni 385, yayin da ya lashe kofin Bundesliga sau takwas tun bayan da ya koma Bayern Munich daga Marseille a shekarar 2007.