rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wenger yayi bankwana da Arsenal

media
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Ian Walton/Reuters

Mai horar da Arsene Wenger, ya yi bankwana da kungiyar cikin yanayi na kewa bayan kammala wasan da Arsenal din ta lallasa kungiyar Burnley da kwallaye 5-0 a filin wasa na Emirates.


Wasan na jiya ya baiwa Arsene Wenger damar samun nasarar jagorantar kungiyar ta Arsenal samun nasara a wasanni 475 daga cikin wasanni 826 da kungiyar ta buga a karkashinsa a gasar Premier.

Wenger ya fara jagorantar Arsenal a wasan farko da ta lallasa kungiyar Blackburn Rovers da kwallaye 2-0 a flin wasa na Ewood Park.

A jimlace cikin cikin shekaru 22 da ya shafe yana horar da Arsenal, Wenger ya jagoranci kungiyar lashe kofunan gasar Premier 3 da kuma kofunan gasar FA 7.

Magoya bayan kungiyar Arsenal ba zasu manta da kakar wasa ta shekarar 2003/2004 ba, lokacin da kungiyar ta kammala baki dayan wasanninta a ba tare an samu nasara akanta ba a karkashin mai horarwa Arsene Wenger.