rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Arsenal zata bayyana magajin Wenger

media
Arsene Wenger, yayin bankwana da magoya bayansa. Reuters

Shugabancin kungiyar Arsenal ya ce nan wani gajeren lokaci, zai bayyana sunan sabon mai horar da kungiyar da zai maye gurbin Arsene Wenger, wanda ya rage wasanni biyu ya kammala bankwana da kungiyar.


Koda yake babu wa’adin da kungiyar ta tsayar na bayyana sabon kocin, an sa ran bayyanar magajin Wenger kafin fara wasannin gasar cin kofin duniya a wata mai kamawa wato 14 ga watan Yuni.

Daga cikin sanannun masu horar da kwallon kafar da ake sa ran zasu iya karbar jagorancin kungiyar ta Arsenal akwai tsohon kocin Barcelona Luis Enrique, mai horar da Juventus Massimiliano Allegri, da kuma Carlo Ancelotti.

A bangaren tsaffin ‘yan wasan Arsenal da ke takarar mukamin horar da kungiyar akwai Mikel Arteta and da kuma Patrick Vieira.