rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Liverpool ta bayyana bukatar sayen Dembele

media
Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Ousmane Dembélé. REUTERS/Albert Gea

Mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya bada tabbacin cewa ya fara yunkurin sayo dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele.


Dembele mai shekaru 20, ya sauya sheka daga Borussia Dortmund zuwa Barcelona a shekarar bara akan kudi Fam miliyan 95, domin maye gurbin Neymar, wanda ya koma kungiyar PSG da ke gasar Ligue 1 Faransa.

Dembele yayi fama da rauni bayan fara wasa a Barcelona da makwanni kadan, dalilin da ya sashi shafe akalla watanni hudu yana jiyya.

Tun bayan komawarsa wasa ne dai da dama ke kallon har yanzu dan wasan bai samu gurbi a tawagar farko ta kungiyar Barcelona ba, inda aka fi ajiye shi a benci.

Bayan kammala kakar wasa ta bana, ana sa ran Barcelona zata sayi dan wasan gaba na Atletico Madrid Antoine Griezmann, lamarin da ke nuni da kara matsin lamba ga Ousmane Dembele a fafutukar da yake na samun wurin shiga a tawagar kungiyar ta farko.