rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Ba za mu siyar wa Barcelona Griezmann ba"

media
Antoine Griezmann na Atletico Madrid REUTERS/Juan Medina

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Miguel Angel Gil Marin ya caccaki Barcelona bisa kokarinta na dauke Antoine Griezmann daga kungiyarsa.


Gil Marin ya ce, ya gaji da irin halin da Barcelona ke nuna, in da ta ke ci gaba da nacin siyo dan wasan daga Atletico Madrid.

Wannan na zuwa ne bayan a yammacin jiya Talata, kafar radiyon Spain ta rawaito cewa, Barcelona ta shirya ajiye zunzurutun Euro miliyan 100 a matsayin farashin Griezmann .

Sai dai kungiyar ta Atletico Madrid ta bakin shugabanta, ta ce, ba ta da aniyar siyar da dan wasan.