rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Barcelona ta kama hanyar kafa tarihi a La Liga

media
Har yanzu babu wata kungiya da ta doke Barcelona a kakar bana a gasar La Liga ta Spain Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kama hanyar kammala kakar wasannin La Liga ba tare da an doke ta ko sau daya ba, in da a jiya Laraba ta lallasa Villareal da kwallaye 5-1.


A karon farko kenan da Barcelonan ke neman kafa tarihin kammala kakar ba tare da shan kashi a hannun wata kungiya ba.

Yanzu haka Barcelona na da sauran wasannin biyu da za ta yi da Levante da Real Sociedad a cikin makwanni biyu masu zuwa, kafin kafa wannan tarihi.

Tun shekarar 1931-32 raban da a samu wata kungiya a La Liga da ta kammala kaka ba tare da shan kashi ba, in da a wancan lokacin Real Madrid ta kafa wannan tarihin.