rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bajintar Lionel Messi karuwa ta ke yi - Zabaleta

media
Dan wasan kungiyar Barcelona Lionel Messi. REUTERS/Juan Medina

Dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Pablo Zabaleta, ya ce Lione Messi ya fi kwarewa da nuna bajinta a fagen kwallon kafa fiye da yadda yake wasa a lokacin da lashe kyautar gwarzon dan wasa na duniya sau biyar.


A cewar Zabaleta duka Messi ya shafe shekaru biyu ba tare da ya sake lashe kyautar Ballon d’Or ba, har yanzu shi ke gaban takwarorinsa a duniyar kwallon kafa.

Tun bayan kyautar da ya karba a shekarar 2015, Messi ya gaza samun nasara akan abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo wajen sake karbe kyautar ta gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya.

Messi ya taimakawa Barcelona matuka wajen lashe kofunan gasar La liga da Copa del Rey a bana, zalika shi ne kan gaba wajen yawan jefa kwallaye a gasar La liga, inda yake da 34, abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo yana da kwallaye 25.

A ranar Lahadi Barcelona zata yi tattaki zuwa gidan Levante, daga bisani kuma ta karbi bakuncin Real Sociedad a gida.

Idan Barcelona ta yi nasarar a dukkanin ragowar wasannin biyu, zata kafa tarihin zama kungiya a gasar La liga da ta kammala wasanninta a kakar wasa ba tare da an samu nasara akanta ba.