rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ronaldo ya nemi karin albashi

media
Shahararren dan wasan kwallon kafa na Real Madrid Cristiano Ronaldo. REUTERS/Paul Hanna

Cristiano Ronald ya nemi kungiyarsa ta Real Madrid ta kara masa albashin da yake karba zuwa euro 500,000 a mako daya.


Ronaldo ya nemi karin ne bisa sharadin idan har ya taimakawa kungiyar lashe kafin gasar zakarun turai karo na uku a jere, za a tabbatar masa da Karin albashin.

Dan wasan dai yana neman yin kafada da kafada ne da abokin hamayyarsa Lionel Messi, wanda a yanzu shi ne yafi kowane dan kwallon kafa yawan albashi.

Rahotanni yiwuwa bukatar ta Ronaldo ta haddasa rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan wasan Real Madrid domin akwai yiwuwar ya sake yin barazanar barin kungiyar muddin aka ki sauraron bukatarsa.