rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Premier League Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mai yiwuwa Arteta ya maye gurbin Arsene Wenger

media
Mikel Arteta ya bugawa Arsenal wasanni tsawon shekaru 5. Reuters

Bayanai sun ce mataimakin mai horar da kungiyar Manchester City, Mikel Arteta na kan gaba, a tsakanin takwarorinsa da ake fatan ganin sun karbi ragamar horar da kungiyar Arsenal.


Arteta wanda tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal ne, ya bugawa kungiyar wasanni 150, kafin daga bisani ya zama mataimakin mai horar da kungiyar Manchester City a shekarar 2016.

Har yanzu dai babu tabbacin wanda zai maye gurbin Arsene Wenger daga hukumar Arsenal, sai dai kungiyar ta jaddada kwarin gwiwar bayyana sabon mai horar da ita kafin fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yuni mai zuwa.

Sauran wadanda ake dangantawa da karbar horar da kungiyar ta Arsenal sun hada da tsohon mai horar da Barcelona Luis Enrique, da kuma mai horar da Juventus Massimiliano Allegri.