rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Bundesliga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Stuttgart ta kawo karshen yunkurin Munich na kafa tarihi a Bundesliga

media
Mai horar da kungiyar Bayern Munich Jupp Heynckes. REUTERS/Michaela Rehle

Mai horar da Bayern Munich Jupp Heynckes ya kawo karshen aikinsa na jagorantar kungiyar a gasar Bundesliga da fuskantar rashin nasara ta farko a gida, karo na farko cikin sama da shekaru 2.


Kungiyar Stuttgart ce ta lallasa Munich da kwallaye 4-1 a wasan karshe na gasar Bundeliga a kakar wasa ta bana.

Rashin nasarar ta kawo karshen cigaba da jera wasannin da Bayern Munich ta ke yi har 37 ba tare da an samu nasara akanta ba.

Sai dai duk da wannan rashin nasara, an mikawa Bayern Munich kofin gasar Bundesliga da ta lashe karo na shida a jere.

A ranar Asabar ta mako mai zuwa mai horar da Munich Heynckes zai jagoranci kungiyar a wasan karshe kafin ya yi ritaya, inda zasu fafata da Eintracht Frankfurt a wasan karshe na cin kofin Jamus.