rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Salah ya sake kafa tarihi a Ingila

media
Mohamed Salah na Liverpool REUTERS/Andrew Yates

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya sake kafa wani sabon tarihin zura kwallo a gasar firimiyar Ingila, in da kuma ya taimaka wa kugiyar wajen samun gurbi a gasar cin kofin zakarun Turai a kaka mai zuwa.


Salah wanda ya fi zura kwallaye a kakar bana a firimiyar ta Ingila, ya ci wa Liverpool kwallo guda a fafatawar da suka doke Brighton da ci 4-0 a jiya Lahadi.

Salah ya karbi kyauyar takalmin zinari a matsayinsa na wanda ya fi zura kwallaye a bana a gasar, sannan ita kanta Liverpool ta karrama shi a matrayin gwarzonta na shekara.

A bangare guda ana iya cewa, Liverpool din ta tsallake rijiya da baya, domin kuwa da ta yi sakacin rashin samun nasara akan Brighton, sannan kuma Chelsea ta doke Newcastle, to da babu shakka Liverpool din za ta rikito daga matakin kungiyoyi hudu da ke saman teburin gasar.