rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan wasan da za su wakilci Najeriya a Rasha

media
Wasu daga cikin tawagar 'yan wasan Najeriya Reuters/Peter Cziborra

Mai horar da tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr ya fitar da jerin sunaye na wucen gadi na 'yan wasa 30 da za su wakilcin kasar a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci nan da kwanaki 30 masu zuwa.


Daga cikin ‘yan wasan akwai Mikel Obi da Abdullahi Shehu da Elderson Echiejile da kuma Leon Balogun.

Har ila yau akwai ‘yan wasan tsakiya kamar Ogenyi Onazi da Oghenekaro Etebo da kuma yan wasan gaba, irinsu Ahmed Musa da Victor Moses.

Rohr bai kuma manta da ‘yan wasa kamar su Wilfred Ndidi da Kelechi Iheanacho da kuma Moses Simon da Alex Iwobi ba.

Najeriya wadda ke cikin rukunin D za ta kara da kasashen Argentina da Crotia da kuma Iceland kuma a ranar 16 ga watan Juni ne za ta fara wasa da Croatia a filin wasa na Kaliningrad.

GA CIKAKKEN JERIN SUNAYEN 'YAN WASAN

MASU TSAREN BAYA:

William Troost-Ekong,

Leon Balogun,

Ola Aina,

Kenneth Omeruo,

Bryan Idowu,

Chidozie Awaziem,

Abdullahi Shehu,

Elderson Echiejile,

Tyronne Ebuehi and

Stephen Eze.

'YAN WASAN TSAKIYA

 John Mikel Obi,

Ogenyi Onazi,

John Ogu,

Wilfried Ndidi,

Uche Agbo,

Oghenekaro Etebo,

Joel Obi

Mikel Agu

'YAN WASAN GABA

Odion Ighalo,

Ahmed Musa,

Victor Moses,

Alex Iwobi,

Moses Simon,

Kelechi Iheanacho,

Junior Lokosa

Simeon Nwankwo

MASU TSAREN RAGA

Ikechukwu Ezenwa

Daniel Akpeyi

Francis Uzoho

Dele Ajiboye.