rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tennis: Serena Williams ta koma ta 454 daga mataki na 1

media
Tsohuwar lamba 1 a fagen wasan kwallon tennis ajin mata a duniya Serena Williams, yar kasar Amurka. REUTERS/Kevin Lamarque

Daga matakin kwararriya ta 1 a duniya a fagen wasan kwallon tennis, a yanzu Serena Williams ta koma ta 454.


Wannan sabon matsayi da Serena ta tsinci kanta a ciki yazo ne, bayan soma gasar tennis ta French Open a ranar Litinin da ta gabata, wadda zata gudana zuwa 10 ga watan Yuni a filin wasa na Roland-Garros da ke birnin Paris.

Sai dai duk da wannan koma baya Serena ta ce tana da kwarin gwiwar nuna bajinta a wannan gasa da ake yiwa lakabi da Grand Slam, wadda ita ce karo na 24 da zata fafata cikinta.

A lokacin da Serena Williams ta tafi hutun haihuwa a watan Janairu na shekarar bara, ita ce ‘yar wasan tennis ta farko a duniya ajin mata, sai dai bayan dawowarta ta gaza rike kambin nata, saboda rashin murmurewa sosai.

‘Yar uwar Serena wato Venus Williams, ke a matsayi na 9 a duniya wajen shahara a fagen kwallon ta tennis.