rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Spain Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Real Madrid ka iya rasa 'yan wasa 5 a kaka mai zuwa

media
Kochiyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na shirye-shiryen sayar da akalla ‘yan wasa 5 don harhada kudin da za ta sayo Neymar Junior daga PSG ta Farasan da kuma Mohamed Salah dan kasar Masar da ke taka leda a Liverpool.


‘Yan wasan da ake saran za su tafi a wannan kaka sun hadar da Gareth Bale, Kiko Casilla Dani Ceballos da kuma Borja Mayoral yayinda wasu jaridun wasanni ke karawa da Christiano Ronaldo ko da dai Kochin Kungiyar Zinadine Zidane ya ce suna fatan sauya shawarar Ronaldon dan Portugal.

Zidane dai bai nuna damuwa da kalaman Gareth Bale na barin Madrid ba duk da cewa ya zura kwallaye biyu a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai wanda ya kai su ga samun nasara dage kofin sau uku a jere.

Neymar Junior dai shi ne dan wasa mafi tsada a kakar 2017 ta watan Agusta kuma dama tun tuni Real din ta nuna sha’awar sayensa daga Barcelona tun kafin zuwansa PSG amma rashin tagazawa ya sanya PSG saye shi tun a wancan lokaci.

Sai dai wata majiya na cewa har yanzu fa Neymar din dan Brazil bai tsaida shawarar yiwuwar komawarsa Madrid ba.

To a bangare guda kuma Mohammed Salah dan kasar Masar da ke taka leda a Liverpool na gab da samun tayi daga kungiyar kwallon kafa ta Madrid kasancewar daga cikin ‘yan wasan da kungiyar ke fatan saye da zarar an bude kasuwar cinikayyar ‘yan wasa ta bana, ko da dai ana burin Madrid din na saye Salah ka iya gamuwa da tankarga ganin yadda ta kaya a wasan karshe na lashe kofin zakarun Turai inda ake zargin kaftin din Real Sergio Ramos da jiwa Salah ciwo da gan-gan wadda yanzu haka zai yi jniyar makwanni uku.

Ita ma dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na shirin zuba makudan kudade don sayen dan wasan dan kasar Masar mai shekaru 25 da tauraruwarsa ke haskawa a wannan kaka.