rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis Faransa Paris

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Djokovic ya kai zagaye na 3 a gasar Roland-Garros

media
Shahararren dan wasan kwallon tennis Novak Djokovic. Reuters / Gonzalo Fuentes

Tsohon zakaran gasar kwallon tennis na duniya Novak Djokovic dan kasar Serbia, ya samu kaiwa zagaye na 3 a gasar French Open ko Roland Garros da ke gudana a Faransa karo na 13 a jere.


Djokovic ya lallasa Jaume Munar dan Spain da 7-6, 7-1, 6-4 da kuma 6-4 a fafatawar da suka yi jiya Laraba.

Sai dai a yanzu Djokovic ya rasa matsayinsa na zama kan gaba a tsakanin ‘yan wasan tennis na duniya, inda yake mataki na 22, koma baya mafi tsauri da ya taba fuskanta tun a shekarar 2006 a lokacin da yake dan shekara 19.

A shekarar 2017 da ta gabata raunin da Djokovic ya samu ya tilasta masa ficewa daga gasar Wimbledon da ta gudana a Birtaniya, wanda kuma bai samu dawowa fagen wasa ba, sai a farkon watan Janairu na wannan shekara, hakan ya taka rawa wajen rashin komowarsa da karfi fagen wasan na Tennis, a dalilin tiyatar da aka yi masa.

A bangaren mata kuwa a dai gasar ta French Open ko Roland Garros, Caroline Wozniacki ta Denmark ‘yar wasa ta 2 a duniya mafi kwarewa a wasan na Tennis, ta kai zagaye na 3, bayan lallasa Georgina Garcia Perez ta Spain da kwallaye 6-1 da kuma 6-0.