rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Argentina

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Messi na gaf da kafa tarihi a yankin Kudancin Amurka

media
Lionel Messi. Reuters/Henry Romero

Lionel Messi ya zarta tsohon gwarzon dan kwallon duniya Ronaldo Nazario na Brazil wajen zama daya daga cikin ‘ya wasan da suka fi yawan zura kwallaye a tarihin yankin Kudancin Amurka.


A halin yanzu Messi yana bukatar sake zura wasu kwallayen 14 ne kawai, domin zama wanda ya fi kowa yawan zura kwallon, a tsakanin ‘yan wasan na kasashen Kudancin Amurka.

Kwallaye 3 da Messi ya ci a wasan sada zumuncin da suka lallasa Haiti da 4-0, ya bashi damar kafa tarihin cin kwallaye 64 jimilla, yayinda Ronaldo Nazario na Brazil, ya ke da kwallaye 62 a lokacin da ya yi ritaya.

A yanzu Pele ne kadai ke gaban Messi a tsakanin 'yan shahararrun 'yan kwallon kafar na yankin Kudancin Amurka mai kwallaye 77 jimilla a tarihinsa na bugawa kasarsa ta Brazil wasanni.