rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guardiola na nuna bambancin kan bakaken fata - Yaya Toure

media
A cewar Toure Guardiola na son ya bara Man City ne saboda kalar fatarsa amma ba don wani abu ba. OLI SCARFF / AFP

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure ya zargi Pep Guardiola da nuna bambanci kan ‘yan kwallo bakaken fata, inda ya ce yafi nuna fifiko karara akan fararen fata ko da kuwa basu kai kwarewar bakaken ba.


Toure dan Ivory Coast mai shekaru 35 wanda ke wannan batu yayin tattaunawarsa da wata mujallar wasanni da ake wallafawa a Faransa, ya ce Guardiola na son ya bar Man City ne saboda kalar fatarsa, inda a wannan kaka wasanni 17 kadai ya bashi damar takawa.

Toure dai ya bar City ne bayan shafe kakar wasa uku a lokacin da Guardiola ya zama kociyanta amma kuma suka kara hadewa a City.

Toure ya taka leda a wasanni 319 cikin kaka 8 inda ya dage kofunan Firimiya 3 FA 1, sai dai yana korafin yadda Guardiola ya hana mishi yin bankwana kamar yadda Iniesta na Barcelona da kuma Buffon na Yuventus suka yi a wannan kaka.