rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Salah zai buga wa Masar wasar cin Kofin Duniya

media
Salah zai buga wa Masar wasar cin Kofin Duniya Phil Noble/Reuters

An bayyana saka kwararren mai kai harin nan na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah daga cikin ‘yan wasar da za su buga wa kasar Masar gasar cin Kofin kwallon Kafa ta Duniya a wannan shekarar ta 2018.


Kungiyar shirya wasanni ta kasar Masar ta ce an saka Mohammed Salah cikin masu buga wa kasar ne a yayin da yake murmurewa daga jinyar raunin da ya samu a kashin Kamfalin Kafadarsa a wasar karshe ta zakarun nahiyar Turai.

An dai yi jinyar Salah ne a wata Assibiti da ke a Valencia ta kasar Andalus wato Spain kenan, kuma yana cike da fatar ganin ya buga wa kasarsa wato Masar kuma a fitarsa ta farko da zai yi a gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya, tun daga 1990.

A ranar Larabar da ta gabata dai hukumar kwallon kafa ta Duniya ta ce Salah zai kwashe sama da makwanni 3 a rataye, abinda ke nuni da cewar mai nyuwa ba zai samu shiga cikin ‘yan wasar kasar Masar da za su buga da kasar Uruguay ba a ranar 15 ga watan Yuni, sai wasar da za su yi da Rasha ran 19 ga watan Yuni sannan da Saudi Arebiya ran 25 ga watan Yuni.

Yanzu haka dai Salah na da gwala-gwalai 44 ne da ya jefa a kakar wasar da ta gabata a dukkanin wasannin da Club dinsa na Liverpool ya buga, kuma an tilasta masa fita daga wasar ne bayan da Jagoran ‘yan wasa na Real Madrid Sergio Ramos ya yi masa keta.