rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Man United za ta saye Diogo Dalot dan Portugal daga Porto

media
Tawagar kungiyar kwallon kafar Portugal. JOSE MANUEL RIBEIRO / AFP

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya amince da sayen dan wasan baya na kungiyar Porto, Diogo Dalot kan yuro miliyan 19.


Dalot dan Portugal mai shekaru 19 wasanni 7 kadai ya fito a bangaren ‘yan wasan Portugal manya amma aka bayyana shi a matsayin dan wasan baya mafi hazaka a bana ajin kananun yara na bana.

Tuni matashin dan wasan ya amince da rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 da Man United din wadda za ta kai shi nan da shekarar 2023.

Kafin rattaba hannunsa kan kwantiragi da Porto, Dalot ya wakilci tawagar ‘yan kwallon Portugal ‘yan kasa da shekaru 15 da kuma ‘yan kasa da shekaru 21 inda a wannan karon aka shigar da shi tawagar manya.

A cewar Mourinho, Dalot shi ne dan wasa mafi hazaka a nahiyar Turai.

Yanzu haka dai Dalot ne dan wasa na biyu da United ta amince da sayen shi a wannan kaka, bayan Shakhtar Donetsk da ta sanar da sayenshi jiya kan Yuro miliyan 47.