rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Isra'ila Falasdinawa FIFA

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Isra'ila ta zargi Falasdinawa da firgita 'yan wasan Argentina

media
Lionel Messi a tsakiyar takwarorinsa 'yan wasan kasar Argentina bayan kammala wasa da Peru, na neman cancantar halartar gasar cin kofin duniya a Buenos Aires, wanda aka tashi 0-0, a watan Oktoba na 2017. AFP

Hukumar kwallon kafa ta Isra’ila, ta ce zata shigar da karar takwararta ta yankin Falasdinu gaban hukumar FIFA, bisa zarginta da tursasawa tawagar kwallon kafar Argentina, soke wasan sada zumuncin da aka shirya zasu buga a birnin Kudus, ranar Asabar mai zuwa.


Shugaban hukumar kwallon kafa ta Isra’ila Rotem Kamer, ya zargi takwaransa na Falasdinu Jibril Rajoub da yin barazana ga rayuka da kuma iyalan ‘yan wasan Argentina, duk da cewa babu wata kwakkwarar shaida kan zargin da ya bayyana.

Rahotanni sun ce shugaban hukumar kwallon kafa na yankin Falasdinu, Jibril Rajoub, ya bukaci Lionel Messi da ya jagoranci ‘yan wasan Argentina wajen kauracewa wasan sada zumuncin, in kuwa ba haka, zai umurci Falasdinawa masoya kwallon kafa su kone dukkanin rigunan da ke dauke da sunansa.

Sai dai a nata bangaren hukumar kwallon kafa ta Argentina ta ce, ta soke buga wasan sada zumuncin da Isra’ila ne a birnin na Kudus, saboda gano cewar wasan na tattare da manufar siyasa.