Ozil ba zai taka leda a gasar cin kofin duniya ba
Dan wasan gaba na Arsenal Mesut Ozil ba zai samu damar bugawa kasarsa Jamus wasan cin kofin duniya ba, bayan raunin daya samu yayin wani wasan sada zumunta da Austria ta lallasa su da ci 2 da 1 ranar asabar din da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Haka zalika Ozil mai shekaru ba buga wasan sada zumunci da Jamus ta kara da Saudi Arabia a yau ba, wasan.
A cewar shugaban tawagar kwallon kafar ta Jamus Oliver Bierhoff dan wasan zai iya maleji ya doka wasannin cin kofin duniyar amma baya son takurawa lafiyarsa.
Ozil, wanda ya kammala kakar wasa ta bana da rauni a baya, ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya shiryawa gasar cin kofin duniyar wadda za su hadu da Mexico a karon farko ranar 17 ga watan nan kafin daga bisani su fafata da Korea ta kudu da kuma Sweden wadanda dukkaninsu ke a rukunin F.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu