rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Victor Moses na shan suka kan rashin nasarar Super Eagles

media
Victor Moses dan wasan Najeriya da ke taka leda a Chelsea. Reuters/Andrew Yates

Dan wasan gaba na Najeriya Victor Moses na ci gaba da shan suka daga magoya bayan kungiyar kwallon kafar kasar bayan gagarumar rashin nasarar da kasar ke fuskanta a dai dai lokacin da gasar cin kofin duniya ke kara karatowa, inda ko a jiya Jamhuriyar Czech ta lallasa ta da ci 1 da nema.


Wasu dai na ganin Moses bai yi katabus a wasan na jiya ba inda su ke ganin kamar yana nunawa kwallon isa, da takama amma kuma ya gaza taimakawa a zura ko da kwallo guda a raga.

A cewarsu ko Mikel Obi da ya ke Striker ya rika bin kwallon a wasan na jiya amma shi Moses sai ya tsaya a baya kawai yana jiran kwallon ta zo ta same shi ya zura a raga.

Cikin wasannin baya bayan nan kama daga wanda Super Eagles din ta fita dama wanda ta karbi bakonci babu ko daya da ta yi nasara inda ta ke shirin fuskantar kasashen Argentina Iceland da kuma Croshiya a rukunin D na gasar ta cin kofin duniya a Rasha.