Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai yuwa Salah ba zai buga wa Masar wasar farko ba a Rasha

Yanzu haka ana shakkun da wuya shanararren dan wasar nan dan kasar Masar mai buga wa Club din Liverpool Mohamed Salah ya samu buga wa kasasrsa wasar farko a gasar wasar kwallon kafa ta Duniya da ake shirin farawa a Rasha.

Mohamed Salah a lokacin da ya samu rani a Kafada
Mohamed Salah a lokacin da ya samu rani a Kafada REUTERS/Phil Noble
Talla

Akwai babbar ayar tambaya akan ko shahararren dan wasar nan Mohamed Salah da kasar Masar mai buga wa Club din Liverpool zai samu buga wa kasarsa wasar ta cin Kofin kwallon Kafa ta Duniya da za su buga tsakaninsu da kasar Uruguay a Rukuni na [A] ranar Jumu’a a can Rasha.

Wannan kuwa saboda labarin da ke fitowa a can kasar na cewar Likitan Club din na kasar Masar Mohamed Abou al-Ela ya sake kwantar da shi Mohamed Salah a gadon Assibiti a ci gaba da jinyar kashin kamfalin kafadarsa da yake yi.

Idan ko hakan ta kasance, to masu sha’awar ganin wasar Mohamed Salah da dam aba za su ji dadi ba, musamman lura da yanda yake taka Leda a wasanninsa, kuma wannan muhimmiyar dam ace ga Salah ya buga wa kasasrsa wasar cin Kofin Duniya kuma a rukunin farko

Mohamed salah dai zakakurin dan wasa ne da ya zura gwala-gwalai 44 wa Club dinsa wato Liverpool a kakar wasar bana.

Amma mai tsaron gidan kasar Uruguay Fernando Muslera da kansa ke fatar Allah ya kaddara da Mohamed Salah ne za su buga wasar, yana cewar shi yana sha’awar ya ga kwararren dan wasa na taka leda koda yake Masar ce za ta kalubalancesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.